Kungiyar Kula da Kananan Wiki

This page is a translated version of the page Small Wiki Monitoring Team and the translation is 93% complete.
Outdated translations are marked like this.
Shortcut:
SWMT

Kungiyar Kula da Kananan Wiki (SWMT) kungiya ce ta editocin Wikimidiya wanda, suke amfani da IRC da sauran kayan aiki, wajen kula da kananan wiki akan batanci, sakonni marasa amfani ko kuma trolling. Akwai nau'rar bot da dama da ke sanar da gyararraki da ake zargi zuwa ga shafukan wiki da SWMT ke kula da su. Don taimakawa, a shiga #cvn-swconnect a IRC. Zaku kuma iya gyara sashen jerin masu amfani da ke kasa don yi rijista don bada gudummawa.

Ma'anar kanana

Kanana a wajen Kungiyar masu Kula da Kananan Wiki za'a iya bayyana ma'anar sa ta hanyoyi da dama. Duk da cewa bots a kan monitar IRC sune shafukan wiki da ke da karancin mukalai kasa da 10,000, wannan ba wai yana nufin cewa su kanana bane a matsayin basu da muhimmanci; sai dai, mun fi so mu kula da shafukan wiki masu girman da ya dace, ta yadda zamu iya tsara matakai wajen tsayar da masu batanci da bayanai marasa amfani wadanda ke bata shafukan wiki da dama en masse, ko kuma su hari kananan wiki saboda suna ga zasu iya gujewa gano su baki daya.

Saboda haka, don Allah kada ku ji haushi idan daya daga cikin mambobin mu ya share gyara a kan shafin wiki dinku, idan sun bayyana kansu a matsayin mambobin SWMT; mun zo ne saboda mun damu da shafin ku na wiki, ba wai don muna ga shafi ne na bayan aji ba.

Yadda ake kula da kananan wiki

  1. Bin diddigin sauye-sauye na baya-baya a shafukan kananan wiki ta hanyar IRC ko kuma SWViewer. Duba Kungiyar Kula da Kananan Wiki/IRC don bayanai.
  2. Kai karar batanci da kuma goge shafi a Global sysops/Bukatu.
  3. Goge batanci.
  4. Kai karar mahadar gyara mara muhimmanci ga Spam blacklist.
  5. Za'a iya samun jerin kananan wiki a nan

Izinin aiki na duk shafuka

Duk wani edita mai kyawawan asali na iya zama mamba na SWMT. Duk da haka, awai izinin duk duniya wadanda ka iya taimakawa. Wannan sun hada da global sysop da kuma global rollback. A taimaka a kula cewa ana bukatar matukar sani na SWMT ga masu neman wannnan izinin.

Akwatin mai amfani

Ana bukatar mambobin SWMT da su kirkiri shafin mai amfani na duniya a Meta, wanda zai rika nunawa a shafukan wiki da suke gyara. A jarraba amfani da alamar Babel a shafukan ku na amfani.

Za ku iya kara wannan akwatin mai amfanin zuwa ga shafin amfanin ku ta hanyar rubuta {{User SWMT}}:

 This user is a member of the Small Wiki Monitoring Team.

Duba kuma