Gamayyar Tsarin Gudanarwa/Tuntuɓa ta 2021/Sanarwa
Gamayyar Tsarin Gudanarwa Kashi na 2
Gamayyar Tsarin Gudanarwa (GTG) ta samar da gamayyar yardadden ɗabi'a ga dukkanin Wikimedia movement da duk sauran manhajojinta. Aikin a yanzu yana a Karo na 2 ne, ta fitar da bayyanannun hanyoyin ƙarfafawa. Zaku iya karanta ƙarin bayani akan dukkanin aikin a shafin aikin.
Kwamitin rubuta Daftari: Kira dan nema
Gidauniyar Wikimedia tana ɗaukar ma'aikatan sakai da su shiga cikin kwamiti ɗin da zasu nemi hanyar ƙarfafa tsarin. Ma'aikatan sakai a kwamitin zasu bayar da tsakanin awa 2 zuwa awa 6 a kowane sati daga ƙarshen Afrilu har Yuli da kuma sakewa a Oktoba da Nuwamba. Akwai muhimmanci na ganin kwamiti ɗin ya haɗa mabanbanta da ɗaukar kowa, da haɗa ƙwarewa daban-daban, ta haɗa ƙwararrun masu bada gudunmawa da sabbi, da wasu da suka samu ko suka yi martani, da kuma waɗanda aka tuhume su akan ƙarya da cin zarafi.
Dan nema da samun ƙarin sani game da yadda gudanarwar take, duba Gamayyar Tsarin Gudanarwa/Kwamitin Daftari.
2021 tuntuɓar al'ummu: Sanarwa da kira ga ƴan sakai / mafassara
Daga 5 Afrilu – 5 Mayu 2021 akwai tattaunawa akan manhajojin da dama akan yadda za'a ƙarfafa tsarin ta UCoC (GTG). Muna neman masu sakai dasu fassara muhimman abubuwa, da kuma taimakawan gudanar da tuntuɓa a harsunan su ko manhajojin su ta amfani da waɗannan muhimman tambayoyi. Idan kuna son ku taimaka da sakai ga ɗaya daga cikin matakan nan, ku tuntube mu acikin kowane irin harshe da kuka fin son amfani da shi.
Domin samun sani sosai game da wannan aiki da sauran tattaunawa dake gudana, duba Gamayyar Tsarin Gudanarwa/2021 tuntuɓa.
-- Xeno (WMF) (magana)