Community Wishlist Survey 2021/Invitation (voting phase)/ha
Binciken fata na Al'umma 2021
Muna gayyatar duk masu amfani da sukayi rijista suyi zabe akan 2021 Community Wishlist Survey. Kuna iya yin zabe daga yanzu har zuwa 21 Disamba don yawan buri daban-daban yadda kuke so.
A cikin binciken, ana tattara sabbin abubuwa da ingantattun kayan aiki don gogaggen editoci. Bayan jefa kuri'a, zamu yi iya kokarin mu don biyan bukatun ku. Zamu fara da wadanda suka shahara.
Mu, Community Tech, muna ɗaya daga cikin ƙungiyoyin Wikimedia Foundation. Muna ƙirƙira da haɓaka gyare-gyare da kayan aikin gyaran wiki. Abinda muke aiki akai an yanke shi ne bisa ga sakamakon binciken Abinda muke aiki akai an yanke shi ne bisa ga sakamakon binciken fata na Al'umma. Sau ɗaya a shekara, zaku iya gabatar da buƙatu. Bayan makonni biyu, zaku iya zaɓar waɗanda kuka fi sha'awar su. Abu na gaba, zamu zaɓi buƙatu daga binciken don aiki akan su. Wasu daga cikin burin na iya samun izini ta hanyar masu haɓaka ayyukan sa kai ko wasu rukunin ƙungiyoyi.
Muna jiran kuri'un ku. Mun gode!