Dokar Halin Duniya / Binciken Shekara / Bayanan Mai jefa kuri'a

This page is a translated version of the page Universal Code of Conduct/Annual review/2025/Voter information and the translation is 97% complete.
Outdated translations are marked like this.
Universal Code of Conduct Coordinating Committee (U4C)

An buɗe ƙuri'a kan canje-canjen da aka gabatar ga ka'idojin aiwatar da doka na duniya (UCoC EG) da Yarjejeniya ta U4C tana buɗe daga 17 ga Afrilu har zuwa 1 ga Mayu 2025 23:59:59 (UTC) ta hanyar SecurePoll. Duk masu jefa ƙuri'a a cikin al'ummar Wikimedia za su sami damar tallafawa ko adawa shawarwari biyar na canji, da raba dalilin. Nemo ƙarin cikakkun bayanai kan umarnin jefa ƙuri'a da cancantar masu jefa ƙuri'a a ƙasa.

Hakanan duba Voting FAQs don bayani kan jefa ƙuri'a.

Tsarin zabe

Idan ka cancanta ka jefa kuri'a:

  1. Yi bitar sauye-sauye da aka bukaci yi. Akwai bukatu guda biyar wanda za'a iya zaba.
  2. Yanke hukunci akan amincewa ko rashin amincewa da kowanne daga cikin bukatun. Idan kana so, kana iya rubuta ra'ayinka dangane da sauyukan da aka bukata yayin kada kuri'ar ka.
  3. Koyi yadda za a yi tattara kuri'un ku tare da SecurePoll.
  4. Jeka shafin Zaɓe na SecurePoll kuma bi umarnin.
  5. Tunatar da sauran mambobin al'ummarku don su jefa kuri'a!

Me ake zabe a kai?

Bayanai guda uku game da UCoC da ake bitarsu duk shekara don manyan gyararraki. Dangane da Yarjejeniyar U4C "zasu rika lura sosai da ra'ayoyi akan kariyar Gidauniya, yanayin tafiyar matsaloli, da kuma bayanai daga al'umma masu jagorantar kawunansu don bayyana kalubale don tafiyar da jagorancin al'ummomi masu zaman kansu yadda ya dace don tursasa bin dokokin UCoC. Danuwowi da aka gano za'a rika rubuta su a fili kowa yana gani a allon U4C, za'a rika magance su dangane da kimarsu, ko kuma a sanya su teburi a yayin bitar UCoC na duk shekara." Da kuma Ka'idojin Tursasawa (Misali} an sanar cewa "Dangane da shawarar Majalisar Amintattushekara daya bayan tabbatar da Tursasa Dokoki, Gidauniyar Wikimidiya zata gudanar da tuntubar jama'a da kuma sake duba Dokokin Tursasawa na UCoC." Canji ga UCoC na buktar tabbatarwa daga Majalisar Amintattu.

Me yasa za ku yi zabe?

Yana da muhimmanci cewa Kwamitin Shiryawa na Tsarin Dokokin Bai-daya ("U4C") ya yi aiki daidai da tsarin jagorancin al'ummomi kuma ya bayyana darajar al'umma. Ta haka, yana da muhimmanci cewa UCoC ya cigaba da bayyana darajar al'umma kuma ya tabbatar da U4C yana a matakin da ya dace don nuna al'ummomi.

Yadda ake zabe

 
Misali na kuri'ar SecurePoll. Lura musamman cewa votewiki na iya ba da shawarar cewa ba a shigar da ku ba. Zaɓin ku har yanzu zai ƙidaya.

Ku taimaka kun karanta wannan sashin kafin zuwa Securepoll don koyo akan bayanai da zasu taimaka don fuskantar zabe cikin sauki.

Katin zaben zai bayyana kowanne kowanne daya daga cikin sauyin da aka bukata, kuma su samar da damammaki ga kowanne: "Rashin amincewa" da "Amincewa".

  • Za'a samar da akwatin "Tsokaci" don ku bar karin bayanai dangane da wani damuwa da kuke da shi tattare da ka'idojin.
  • SecurePoll zai sanar da ku cewa an yi rikodin kuri'ar ku.
  • Kuna iya sake jefa kuri'a a zaben. Ya sake rubuta kuri'un da kuka yi a baya. Kuna iya yin hakan sau da yawa kamar yadda kuke so.

Ku je SecurePoll a kan votewiki kuma ku jefa kuri'unku


Ta yaya za a tantance sakamakon zaben?

Za a buƙaci ƙofar sama da kashi 60% na goyon baya ga masu amfani da suka halarci don ƙaddamar da canji don wucewa.

Shin za'a shigar da wasu mutane daga wajen Gidauniyar Wikimidiya a wajen tantance kuri'u don tabbatar da inganci?

Za a binciki sakamakon kada kuri'ar kan rashin bin ka'ida ta a kalla uku wadanda ba ma'aikatan Wikimedia ba wadanda ke da gogewa a tsarin kada kuri'a da tabbatarwa. Za a sanar da masu tantance kuri'u daga baya.

Cancantar Zaɓe

Duk editoci masu rijista wanda suke da iyakan ayyuka da ake bukata, afiliyet da kuma ma'aikata Gidauniyar Wikimidiya da masu kwantiragi (wadanda aka dauka aiki kafin 6 ga watan March 2025), da kuma amintattuh Gidauniyar Wikimidiya na yanzu da na baya, zasu samu damar yin zabe a kan da sauye-sauyen da aka bukata ga Dokokin Tursasawa da kuma Yarjejenita a Securepoll.

Idan ka yi imanin cewa kun cancanci yin zabe amma SecurePoll bai bari ka shiga ba, a tura sakon email ca@wikimedia.org don janyo hankali.

Editoci

Kuna iya jefa kuri'a daga kowane asusun rajista da kuka mallaka a kan wiki na Wikimedia. Kuna iya jefa kuri'a sau ɗaya kawai, ba tare da la'akari da asusun da kuka mallaka ba. Don samun cancanta, wannan asusun dole ne:

  • ba'a taba bulokin ba a shafi fiye da guda daya;
  • kuma kada ka kasance bot;
  • kuma ka yi akalla gyare-gyare 300 kafin 6 Maris 2025 a fadin Wikimedia wikis;
  • kuma ka yi akalla gyare-gyare 20 a duk faɗin shafukan wiki na Wikimidiya tsakanin 6 ga Satumba 2024 da 6 ga Maris 2025.